Saura kiris na koma Arsenal - Barton

Joey Barton
Image caption Joey Barton yanzu shi ne kyaftin din Queens Park Rangers

Sabon kyaftin din Queens Park Rangers Joey Barton ya ce saura kadan ya koma Arsenal a watan da ya gabata.

Amma dan wasan mai shekaru 29, wanda a lokacin yana Newcastle, ya ce rikicin da ya faru a canjaras din da Arsenal ta yi da Newcastle wanda ya kai ga baiwa Gervinho jan kati shi ne ya kawo tsaiko.

An soki Barton da yin langwai lokacin da alkalin wasa Peter Walton ya baiwa dan wasan jan kati.

"Da ban buga wasan mu da Arsenal ba, da tuni na koma cikinsu," a cewar Barton.

"Mun tattauna sau da dama da koci Arsene Wenger, amma hakan yana da banbanci da sanya hannu kan yarjejeniya.

"Lamarin Gervinho ya faru don haka babu abinda zan iya yi a kai. Idan ya sake faruwa, zan sake tunani kan yadda zan bullo masa.