Claudio Ranieri ne sabon kocin Inter

Claudio Ranieri Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Claudio Ranieri ya bar Roma a watan Fabrerun bana

An nada tsohon kocin Chelsea Claudio Ranieri a matsayin sabon kocin Inter Milan inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu.

Sanarwar ta biyo bayan korar da aka yi wa Gian Piero Gasperini ranar Laraba da safe.

An kori Gasperini ne bayan ya sha kashi a wasanni hudu daga cikin biyar da ya buga.

Wannan ne aiki na farko da Ranieri ya samu tun bayan da ya bar Roma a watan Fabreru sakamakon rashin nasara.

"Claudio Ranieri shi ne sabon kocin Inter," a cewar wata sanarwa da kulob din ya fitar ranar Alhamis.

A hannun Gasperini, Inter ta sha kashi da ci 3-1 a hannun Novara ranar Talata, kafin sannan Palermo ta doke ta a Serie A, Trabzonspor a gasar zakarun Turai, da kuma AC Milan a Italian Super Cup.

Sai dai shi ma tsohon kocin na Juventus Ranieri bai taka wata rawa ta azo a gani ba a baya, inda ya lashe kofin Italian Cup a 1996 da Fiorentina da kuma Spanish Cup da Valencia bayan shekaru uku.