BBC ta bankado badakala a London 2012

BBC ta bankado badakala a London 2012 Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Hukumar damben WSB ta musanta wannan zargi

Shirin Turanci na BBC Newsnight, ya ce akwai shaidun cewa Hukumar kula da wasan dambe ta duniya ta karbi kudi daga Azerbaijan domin bata zinare a wasannin Olympic da za a yi badi a birnin London.

Shirin ya ce wani babban jami'i a Hukumar damben WSB ya ce kudin wani bangare ne na yarjejeniyar cewa za a baiwa 'yan damben Azerbaijan tabbacin lashe zinare biyu a gasar wasannin Olympics ta London 2012.

Masu shirya gasar damben a Olympics, AIBA, sun amince cewa wani dan kasar Azerbaijan ya biya dala miliyan 9 ga daya daga cikin wasannin da ya ke shiryawa.

Amma sun musanta cewa an yi wani alkawari kan sakamakon gasar ta Olympics.

Lauyoyin hukumar kuda da wasan dambe na matasa (AIBA), sun shaida wa BBC cewa duk wani zargi mai kama da wannan "ba shi da tushe".

Kuma wannan matsayin ya samu goyon bayan shugaban AIBA Dr Ching-Kuo Wu, wanda ya shaida wa Newsnight cewa "zargin ba gaskiya ba ne".

Ya kuma kara da cewa Hukumar "WSB na gudanar da al'amuranta cikin gaskiya kuma a fayyace".

Sai dai ya ce AIBA ba ta goyon bayan cin hanci da rashawa, don haka zai gudanar da cikakken bincike ba tare da bata lokaci ba.