Inter Milan ta farfado,Juventus na kan gaba

AC Milan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption AC Milan ce ta lashe gasar data wuce a Italiya

Bayan shafe makwanni hudu ana buga wasa a gasar Serie A ta Italiya, Juventus ce ke kan gaba a kan tebur da maki takwas tare da Udinese.

A yayinda Inter Milan wacce ta nada sabon koci wato Claudio Raneri ta soma da kafar dama, bayanda Inter din ta samu galaba akan Bologna daci uku da daya.

Sakamakon sauran wasanni:

*Chievo 2 - 1 Genoa *Atalanta 2 - 1 Novara *Cagliari 0 - 0 Udinese *Catania 1 - 1 Juventus *Lazio 0 - 0 Palermo *Siena 3 - 0 Lecce *Bologna 1 - 3 Internazionale *Milan 1 - 0 Cesena *Napoli 0 - 0 Fiorentina