London 2012: Najeriya za ta kara da Morocco

Austin Eguavoen Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Najeriya 'yan kasada shekaru 23 Austin Eguavoen

An rarraba kasashen Afrika takwas da zasu kara da juna a wasan neman gurbin zuwa gasar kwallon kafa na gasar Olympics da za ayi a badi a London.

A watan Nuwamba za ayi fafatawar inda aka rarraba kasashen zuwa rukunoni biyu wato Najeriya da Morocco da Algeriya da kuma Senegal sune a rukuni na biyu.

A rukunin farko kuwa akwai Afrika ta Kudu da Masar da Gabon da kuma Ivory Coast.

Rukunin A: * Masar * Ivory Coast * Afrika ta Kudu * Gabon

Rukunin B: * Nigeria * Algeria * Morocco * Senegal

Kasashe uku na farko zasu tsallake zuwa gasar a London a yayinda kasa ta hudu zata buga wasan kifa daya kwala tsakaninta da wata kasa daga nahiyar Asiyar.