Gidajen talabijin nada karfi a Ingila-Ferguson

Sir Alex Ferguson Hakkin mallakar hoto
Image caption Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce gidajen talabijin nada matukar karfi a harkar kwallon gasar premier ta Ingila.

Ferguson ya shaidawa BBC cewar gidajen talabijin ne ke juya akalar gasar saboda makudan kudaden da suke sakawa a cikin gudanar da gasar.

A cewarsa kulob basuda karfin fada aji akan wasannin da zasu buga kuma hakan ya janyo nakasu ga manyan kulob din dake taka leda a Turai.

Har wa yau, Ferguson din ya ce kulob kulob basa samun kudaden da suke bukata daga wajen gidajen talabijin.

A sabuwar yarjejeniyar dake tsakanin gidajen talabijin da mahukunta gasar premier, United ta samu fiye da fan miliyon sittin a kakar wasan data wuce saboda wasanninta da aka nuna a talabijin.