Wilshere zai yi jinyar watanni biyar

Jack Wilshere Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jack Wilshere ya na taka leda sosai a Arsenal da Ingila

Dan wasan tsakiya na Arsenal Jack Wilshere zai shafe watanni biyar ya na jinya bayan da aka yi masa tiyata a gwiwarsa.

Dan wasan mai shekaru 19 ya samu raunin ne a wasan sada zumuncin da Arsenal ta kara da New York Red Bulls a watan Yulin da ya gabata.

Da farko an yi zaton raunin ba zai haifar da wata jinya mai tsayi ba.

Wata sanarwa da aka buga a shafin intanet na kulob din ta ce: "Muna kyautata zaton Jack Wilshare zai shafe watanni hudu zuwa biyar ya na jinya."

Da farko dan wasan na Ingila ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: "An yi min tiyata kuma komai ya tafi daidai! Zan kwana a asibiti domin a kula da ni, amma baya ga wannan ba ni da wata damuwa!"

Ya kara da cewa "Ina mika godiya ga sakonnin fatan alherin da kuka rinka aiko min - magoya bayan Arsenal. Za mu hadu nan gaba kadan a filin wasa na Emirates."