Ina jin dadin taka leda a Anzhi -Eto'o

etoo Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Samuel Etoo yana murza leda a gasar Rasha

Sabon dan kwallon Anzhi Makhachkala Samuel Eto'o ya ce hukuncinsa na barin gasar Serie A zuwa gasar kwallon Rasha mataki ne na inganta kwallonsa.

Amma kuma masu sharhi akan kwallon kafa na ganin cewar dan kwallon Kamaru ya kawo karshen kwallonsa ne da kanshi.

Eto'o wanda shine wanda yafi kowanne dan kwallo a duniya karban albashi ya ce bai taba mafarkin komawa kwallo a Rasha ba.

Yace"Ina jin dadi a Anzhi koda yake ban taba tunanin komawa kwallo a wannan yankin ba".

A cewar Eto'o rayuwa a Anzhi akwai dadi musamman yadda ake yi musu tafinta tsakaninsu da kocinsu.

A kakar wasa ta bana dai kyaftin din Kamaru din ba zai gasar Zakarun Turai ba amma kuma yanasaran ya cimma burinsa a nan gaba.