Ban ki buga wasanmu da Bayern ba-Tevez

tevez Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana takun saka tsakanin Tevez da Mancini

Dan kwallon Manchester City Carlos Tevez ya karyata zargin cewar yaki amincewa ya buga wasansu da Bayern Munich a gasar zakarun Turai.

Tevez ya fusata kocinsa Roberto Mancini akan nuna rashin sha'awarsa ya buga kwallon bayan ana cin City daci biyu da nema.

A cewar Mancini daga yanzu dan kwallon Argentina ba zai kara bugawa City kwallo ba, amma kuma Tevez ya maida martani akan cewar "ya sadaukar da kanshi akan Man City".

Tevez ya kara da cewar "akwai rudani akan benci shi ya sanya ba a fahimci matsayina ba".

Dan kwallon mai shekaru 27 ya kuma nemi afuwar magoya bayan City saboda abinda ya faru.

Wasan Man City na gaba shine a ranar Asabar tsakaninta da Blackburn Rovers a gasar Premier.