Sunderland ta dakatar da Bramble

bramble
Image caption Titus Bramble

Sunderland ta dakatar da dan kwallonta Titus Bramble bayanda aka tsare bisa zargin ya mallaki haramtaciyyar kwaya sannan kuma nemi cin zarafin wata.

Tsohon dan wasan Newcastle mai shekaru 30 an yi mashi tambayoyi kafin a bada belinsa a ranar Laraba.

Sanarwar da kulob din ya fitar yace"An dakatar da Titus Bramble har sai an kamalla bincikensa".

Titus Bramble ya soma kwallo ne a mafaiharsa Ipswich kafin ya koma Newcastle United akan fan miliyon shida.

Ya koma Wigan Athletic daga bisani ya tafi Sunderland a bara.