CAN 2019: Najeriya za ta shiga a dama da ita

Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gasar ta karshe da Najeriya ta shirya ita ce ta 2000, wacce Kamaru ta lashe

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta ce za ta nemi damar shirya gasar cin kofin kasashen Afrika ta shekara ta 2019 bayan da ta kasa samun ta 2013.

An karbe gasar ta 2013 daga Libya inda aka baiwa Afrika ta Kudu.

Najeriya ta nuna sha'awar daukar bakuncin gasar bayan da aka sanya ta a jerin 'yan ko-ta-kwana lokacin da aka zabi Libya.

"Mun yi iya iyawarmu Allah bai bamu nasara ba, mun karbi sakamakon da zuciya guda, ba za mu ce za mu yi wani abu ba," shugaban NFF Aminu Maigari a hirarsa da wakilin BBC Naziru Mika'ilu.

Da aka tambaye shi cewa Najeriya bata dage ba wajen neman gasar, sai Maigari wanda ya je birnin Alkahira domin halartar babban taron hukumar Caf - ya ce sun yi duk abinda ya kamata.

"Dama an sakamu ne a matsayin 'yan ko-ta-kwana, kuma mun tuna musu, mun rubuta wasiku da dama, amma ba mu ji dadi ba, kuma Caf ba ta yi mana adalci ba."

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tuni Afrika ta Kudu da Libya suka amince su yi musayar gasar ta 2013, inda Libya za ta karbi bakuncin gasar a shekara ta 2017.

Maigari ya ce Najeriya na son shirya wata gasar ta kasashen Afrika - bayan da suka shirya ta 2000 tare da Ghana, sannan ta shirya ta shekarar 1980 ita kadai.

"Muna so mu dauka saboda mun cancanta - kuma za mu iya yi, za mu yi takara da kowacce kasa."

Karin bayani