CAF ta nada El Amrani a matsayin Sakatare Janar

hicham
Image caption Hicham El Amrani

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Afrika wato CAF ta tabbatar da nadin Hicham El Amrani a matsayin sakatare janar din ta.

Kwamitin zartarwar hukumar ce ta yanke wannan shawarar a taronta a birnin Alkahira.

Dan kasar Morocco din mai shekaru 32 ya hade da CAF ne a watan Maris na 2009 a matsayin mataimakin sakatare Janar.

Amrani ya kasance sakataren riko tun watan Oktoban bara bayan tafiyar Mustapha Fahmy na Masar zuwa Fifa a matsayin Darekatan dake kula da gasa.

Har wa yau kafin Amrani ya koma CAF yana aiki ne tare da hukumar kwallon nahiyar Asiya.