Tasirin halayyar Tevez ga makomar kwallon kafa

 Carlos Tevez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tevez ya ki yadda ya motsa jiki domin buga wasan City da Bayern

Halayyar da Carlos Tevez ya nuna ka iya zamowa wani mataki da zai sa kulob-kulob dawowa daga rakiyar manyan 'yan wasansu masu tsada.

Duk da cewa Manchester City ta dakatar da Tevez saboda ya ki amincewa ya taka leda a wasansu da Bayern Munich ranar Talata, masu sharhi da tsofaffin 'yan wasa da dama na ganin ya kamata a kore shi.

Ko da mataimakin shugaban FIFA Jim Boyce ya tofa albarkacin bakinsa, yana cewa zai goyi bayan City idan suka soke kwantiragin Tevez wacce ta kai fan 250,000 a mako.

Ana yi wa manyan 'yan wasa kallon shafaffu da mai, sai dai ana ganin kin karbar umarnin koci ba karamin laifi ba ne.

Tsohon dan wasan Liverpool Graham Sounsess ya bayyana halayyar Tevez da cewa "batanci ne ga kwallon kafa", yayin da mai yi wa BBC sharhi Robbie Savage ya ce: "Idan da shi ne kocin kulob din da dan wasan ba zai kara take leda ba".

Idan har City ta kori Tevez, to babu shakka zai nuna cewa duk tsadar dan wasan, karfin fada-aji na hannun koci da kuma shugabannin kulob.

Kuma hakan zai nuna wata alama musamman lokacin da kulob da dama a Ingila musamman City ke da 'yan wasa kwararru da yawa da ke zaune a benci fiye da wadanda su ke taka leda.