Arsenal ba zata taka rawar gani ba-Dixon

arsnel Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Arsenal

Tsohon dan kwallon Arsenal Lee Dixon ya ce matsalar 'yan kwallon bayan da Gunners ke fama dashi zai iya hana kulob din kasancewa cikin jerin kulob kulob takwas na farko a gasar premier ta Ingila.

Bayan da Tottenham ta doke Arsenal, sai Arsene Wenger ya amince ba zasu iya lashe gasar premier ba amma kuma zasu kasance cikin kungoyoyi hudu na farko a gasar.

Amma a cewar Dixon"Ina tunanin shiga jerin kulob hudu na farko ba zai yiwu ba amma ina ganin watakila su shiga cikin shidan farko".

Ya kara da cewar a halin da ake ciki a yanzu, yadda suke taka leda ba zasu wuce takwas na farko ba.

A kakar wasa ta bana, an doke Arsenal a wasanni hudu cikin bakwai kuma sune na goma sha biyar akan tebur.

'Yan wasan Arsenal masu jinya:

* Thomas Vermaelen * Johan Djourou * Sebastien Squillaci * Laurent Koscielny * Bacary Sagna * Jack Wilshere * Abou Diaby