Kotun CAS ta yi watsi da bukatar Bin Hammam

hamamm Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Muhammed Bin Hammam

Kotun sauraron kararakin wasanni tayi watsi da kokarin Mohammed Bin Hammam na komawa kan kujerar shugabancin hukumar kwallon nahiyar Asiya.

Matakin Hammam na kai kara shine don a cire wanda yake rikon shugaban kwallon Asiya , don shi Hammam din ya koma kan shugabancin kafin a soma sauraron karar da ya gabatar akan FIFA.

A watan Mayu ne aka haramtawa Hammam shiga harkar kwallon kafa na iya tsawon rai sakamakon zargin yayi kokarin sayen kuri'a a matsayin dan takarar shugabancin FIFA.

Sakamakon matakin da Fifa ta dauka akansa, sai dan China Zhang Jilong ya dare kujerar shugabancin hukumar kwallon nahiyar Asiya sannan tare da kasancewa mamba a kwamitin zartarwa na FIFA.

Hammam dai ya nemi yin takara ne da Sepp Blatter akan kujerar shugabancin FIFA kafin ya janye bisa zargin kokarin bada toshiyar baki.