Tevez zai tattauna da mahukunta a Man City

tevez
Image caption Carlos Tevez

Dan kwallon Manchester City Carlos Tevez zai tattauna da jami'an kulob din a ranar Litinin, a cigaba da bincike akan zargin yaki yarda ya buga wasansu da Bayern Munich.

An dakatar da dan wasan na makwanni biyu bayan kocinsa Roberto Mancini yayi zargin cewar Tevez ya ce ba zai buga ba a tsakiyar wasansu na gasar zakarun Turai a makon daya gabata.

Mancini ya ce dan Argentina din mai shekaru 27 ya gama yawo a City, amma kuma Tevez din yace akwai rashin fahimta.

A cikin wannan makonne za a kamalla binciken.

Tawagar lauyoyin kulob din na City na daga cikin wadanda Tevez zai yiwa bayani.