Dama ta karshe ga Amos Adamu

amso
Image caption Amos Adamu

A ranar Talata ne Amos Adamu zai bayyana a gaban kotun sauraron kararrakin wasanni a mataki na karshe don sauya dakatarwar shekaru uku da aka yi masa daga shiga harkar kwallon kafa.

Wannan dai ita ce dama ta karshe ga Amos Adamu, wanda tsohon mamba ne a kwamitin zartarwa na Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa dimin ya wanke kansa.

Wata majiya a kotun ta tabbatarwa da BBC cewa zaman kotun zai dauki tsawon lokaci kuma ana saran samun hukunci bayan an mika bayanan ga duka bangarorin.

Kotun sauraron kararaki wasanni wato CAS za ta ji ba'asin dan Najeriya din akan dakatarwar da aka yi mashi daga kwallo.

Kwamitin da'a na Fifa ya dakatar da Adamu bayan an kamashi da laifin kokarin karbar cin hanci a zaben kasashen da zasu dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 da kuma 2022.

An dakatar da Amos Adamu ne tare da dan Mali Amadou Diakite da kuma dan kasar Tonga Ahongalu Fusimalohi a watan Nuwamban bara.