An yiwa Affelay tiyata,zai yi jinyar watanni 6

affekay Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ibrahim Affelay

Dan kwallon Barcelona Ibrahim Afellay zai yi jinya watanni shida bayan nasarar da aka samu a tiyatar da aka yi masa a gwiwarsa ta hagu.

Sanarwar da Barcelona ta fitar a ranar Talata ta ce ba'a samu tangarda ba wajen yin tiyatar.

Dan kwallon Holland din mai shekaru 25 ya koma Barcelona ne daga PSV Eindhoven a watan Disamba kafin yaji rauni a lokacin horo a watan Satumba.

Daya daga cikin likitocin da suka yiwa Affelay tiyata Ricard Pruna ya ce dan kwallon zai murmure a hankali.

Affelay ya buga wasan Barcelona da Ac Milan da kuma na Osasuna a kakar wasa ta bana.