Umar Abdulmutallab zai koma kotu

Umar Abdulmutallab
Image caption Jami'an Amurka ne suka gabatar da wannan hoton na Mutallab

A ranar Talata ne ake sa ran ci gaba da shari'ar da ake yiwa dan Najeriya Umar Farouk Abdulmutallab kan zargin yunkurin tada bam a wani jirgin saman Amurka a shekarar 2009.

A ranar Kirsimetin shekara ta 2009 ne aka kama Abdulmutallab a kan hanyarsa ta zuwa Detroit a Amurka, inda kuma aka zarge shi da yunkurin tayar da bam a jirgin.

Jami'an tsaron Amurka dai sun ce ya yi kokarin tayar da bom din ne wanda ya boye a wandonsa.

Hankulan jama'a dai za su karkata sosai ne a kan wannan shari'ar da za'a ci gaba da ita kwanaki uku bayan kisan Anwar Al-Awlaqi na kungiyar Al-ka'ida da wani jirgin saman Amurka ya yi a kasar Yemen.

Jami'an hukumar leken asirin Amurkan dai sun sha nanata cewa Anwar Al-Awlaqi na da hannu a yunkurin tada bam din a jirgin saman Amurka a shekarar 2009.

Sun zargi Al-Awlaqi da tunzura Abdulmutallab bayan da suka hadu a kasar Yemen.

Umar Faruk Abdulmutallab na fuskantar hukuncin daurin rai-da-rai ne idan har aka same shi da laifi.