Ihun da aka yi wa Adebayor ya fusata Obilale

Emmanuel Adebayor Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Emmanuel Adebayor yana taka rawa sosai a Tottenham

Tsohon golan Togo wanda ya daina taka leda sakamakon harin da akai musu, ya nemi a hukunta wadanda ke da hannu a ihun da aka yiwa Emmanuel Adebayor a wasan Arsenal da Tottenham.

Wasu daga cikin magoya bayan Arsenal sun yi wa dan wasan Tottenham Emmanuel Adebayor ihu kan harin da 'yan bindiga suka kaiwa tawagar Togo kafin fara gasar cin kofin kasashen Afrika na shekara ta 2010.

"Yin wannan waken ya nuna cewa kamar suna goyon bayan ta'addanci ne," kamar yadda Kodjovi Obilale ya shaida wa shirin BBC na Turanci World Football show.

"An ji min rauni a harin. Ya kamata a hukunta wadannan mutanen."

Ya kara da cewa: "Abin bakincike ne, sun wuce gona-da-iri. Jama'a sun rasa rayukansu. Ni ban san abin da Adebayor ya yi ba? Kawai ya na buga kwallo ne."

An harbi Obilale sau biyu a harin, wanda aka kai lokacin da tawagar Togo ke shiga Angola a ranar 8 ga watan Janairun 2010, kwanaki biyu kafin fara gasar cin kofin kasashen Afrika.

An dai kashe mutane biyu har lahira daga cikin tawagar ta Togo.

Kocin Spurs Harry Redknapp da kuma na Arsenal Arsene Wenger duka sun yi Allah wadai da ihun cin mutuncin da magoya bayan suka yi a wasan da Spurs ta doke Arsenal da ci 2-1.