Uefa ta kaddamar da bincike kan Bulgaria

Uefa
Image caption Uefa na yin Allah wadai da nuna banbancin launin fata

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai Uefa ta fara bincike kan kasar Bulgaria sakamakon abin da ya faru a wasan da kasar da fafata da Ingila a watan da ya gabata.

Binciken zai duba zargin kalaman nuna wariyar launin fata da sauran halayyar rashin da'a da magoya baya suka nuna.

Hukumar Uefa na sa ran yanke hukuncin ko za ta dauki mataki kan kasar ta Bulgaria a ranar 15 ga watan Oktoba.

"Za a fara sauraron ba'asi a ranar 13 ga watan Oktoba, bayan kuma an kammala ne za a sanar da sakamakon," a cewar mai magana da yawun Uefa.

Akwai zargin da ke nuna cewa an yi wa dan wasan Ingila Ashley Young kalaman wariyar launin fata.