Corinthians ba za ta sake neman Tevez ba

Carlos Tevez Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A baya Corinthians ta taba neman Carlos Tevez

Kungiyar Corinthians ta Brazil ta ce bata da aniyar sake neman dan wasan Manchester City Carlos Tevez, kamar yadda Janaral Manajansu Edu ya shaida wa BBC.

A farkon kakar bana Corinthians ta yi yunkurin sayen Tevez kan kudi fan miliyan 35, amma daga karshe cinikin bai yiwu ba.

Dan wasan mai shekaru 27 a yanzu an dakatar da shi na tsawon makwanni biyu a yayin da ake gudanar da bincike bayan da aka zarge shi da kin bugawa kungiyar wasa a karawar da suka yi da Bayern Munich.

"A yanzu babu wani shiri na sake yunkurin sayensa," a cewar tsohon dan wasan Arsenal da Brazil Edu.

"Na fara tunani kan tawagarmu ta kakar wasanni ta 2012 kuma na yi magana da kocinmu kan 'yan wasan da za mu dauka amma batun Tevez bai ta so ba kwata-kwata.

"Muna da sha'awar manyan 'yan wasa kamarsu Tevez, amma sai mun yi tunani kan ko ya dace mu saye shi a lokacin ko kuma a'a. Ba mu yi magana da shi ko kuma wakilinsa ba."