Ba na son doguwar kwantiragi a Barca - Guardiola

Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pep Guardiola ya na taka rawa sosai a Barcelona

Duk da nasarar da ya ke samu, kocin Barcelona Pep Guardiola, ya ce ba ya son sanya hannu kan doguwar kwantiragi a kulob din.

A maimakon haka ya fi son ya rinka kara shekara `dai - `dai domin ya samu tabbaci kan makomarsa.

"Kowacce rana ina tunanin zan iya barin aiki. Na fi dagewa idan na son cewa makomata tana hannu na," kamar yadda ya shaida wa jaridar Sport.

"Akwai damuwa idan ka sanya hannu a kwantiragi mai tsawo. Abin da kake yi zai fita daga ranka, wannan shi ne ra'ayi na."

Kwantiragin Guardiola za ta kare ne a watan Yunin shekara ta 2012 kuma wakilinsa, Jose Orobitg, ya bayyana a 'yan kwanakin da suka wuce cewa ya na farin ciki da zamansa a Barcelona.