Zamu saye Adebayor idan aka rage masa albashi

adebayor Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Emmanuel Adebayor

Kocin Tottenham Hotspur Harry Redknapp ya ce idan Emmanuel Adebayor yanason ya kulla yarjejeniyar dun-dun-dun tare da kulob din, to dole sai an rage masa albashi.

Dan wasan Togo mai shekaru 27 wanda yake matsayin aro a Spurs, ya kasa samun damar bugawa da kulob dinsa Manchester City.

A halin yanzu Adebayor ya zira kwallaye uku cikin wasanni hudun daya bugawa Spurs, kuma Redknapp ya ce yanason ya sayi dan wasan.

Yace"Idan Emmanuel ya cigaba da taka leda yadda yake yi a yanzu, zan so in cigaba da rikeshi".

Ya kara da cewar"amma kuma albashinsa ne matsala".