Zamu cigaba da rike Guardiola a Barca-Rosell

guardiola
Image caption Pep Guardiola

Shugaban kungiyar Barcelona Sandro Rosell ya dauki alkawarin cewa zasu yi iyaka kokarinsu don cigaba da rike Pep Guardiola a matsayin kocin kulob din.

Tun da ya soma jan ragama a Nou Camp a watan Yunin 2008, Guardiola yaki amincewa ya dade yana jagorancin kulob din, inda ya sabunta kwangilarsa ta shekara daya.

Batun makomarsa ya kara jan hankalin jama'a ne bayan da yayi wata tattaunawa a jarida inda yace wata rana zai tafi.

Guardiola yace"Ku dakata, a kullum ina tunanin barin kulob din".

Amma kuma Rosell ya jaddada cewar zasu cigaba rike mutumin wanda ya taimaka musu suka lashe gasar kofin La Liga sau uku a jere da kuma na gasar Zakarun Turai biyu a cikin shekaru uku.

Rosell yace"Shine kocin daya fi kowanne a tarihin kulob din, mutumin kirki ne, zamu tabbatar da cewar bai barmu ba".