Ingila ba zata iya lashe gasar kwallon Turai ba

neville
Image caption Gary Neville

Tsohon dan kwallon Manchester United Gary Neville ya bayyana cewar Ingila bata da karfin da zata lashe gasar cin kofin kasashen Turai da za ayi a badi.

Bayan Ingila ta tashi biyu da biyu tsakaninta da Montenegro a wasan share fage, sai kafafen yada labarai suka soma bayanai akan makomar kasar a lokacin gasar.

Neville ya ce"abinda ya kamata a maida hankali a kai shine ya samo wadanda zasu iya rike kwallo".

Ya kara da cewar a gaskiya tawagar bata da karfi sosai.

Neville ya bugawa Ingila wasanni 85 kafin yayi ritaya.