NFF ta bukaci Siasia ya yi bayani cikin sa'o'i 48

siasia
Image caption Samson Siasia

Hukumar kwallon Najeriya NFF ta baiwa kocin Super Eagles Samson Siasia sa'i'o arba'in da takwas ya bayyana dalilan da suka sanya kasar bata tsallake zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika ba.

A taron gaggawar da ta kira, NFF ta ce Siasia ya bada rubuce abinda ya haddasa wannan abun kunyar da Najeriya ta tashi biyu da biyu tsakaninta da Guinea.

Sanarwar ta ce "dole ne Siasia sai ya bada bayani akan irin mummunar rawar da Najeriya ta taka a kokarinta na tsallakewa zuwa gasar".

Tunda farko dai Samson Siasia ya nemi afuwar 'yan Najeriya akan wannan abinda ya faru.

Najeriya bata fafata ba a gasar cin kofin Afrika a 1986 da 1996 da kuma 1998.