2012:Afrika ta Kudu ta soki CAF akan Nijer

Afrika ta kudu Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Afrika ta Kudu ta shiga damuwa

Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta Kudu-Safa ta kai kara wajen hukumar kwallon Afrika wato CAF akan tsarin yadda kasashe ke samun gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen nahiyar da za ayi a shekara ta 2012.

Bafana Bafana ta nuna rashin gamsuwarta akan yadda Caf ta ce Nijer ta tsallake daga rukunin G duk da cewar Afrika ta Kudu ta zira yawan kwalayen da suka fi na Nijer din.

Sanarwar da Safa ta fitar ta ce "muna shirin kalubalantar wannan matakin da dokokin".

Kasashe ukun dake rukunin wato Nijer da Afrika ta Kudu da Saliyo duk suna da maki tara.