CAN 2012:Morrocco da Sudan suma zasu halarta

caf
Image caption Hukumar CAF ce ke shirya gasar kwallo a Afrika

Kasashen da zasu fafata a gasar cin kofin kasashen Afrika da za ayi a badi sun cika goma sha shida cif cif.

A karshen mako ne aka kamalla wasanni share fagen neman gurbin zuwa gasar.

Kasashen da zasu halarci gasar sun hada da masu masaukin baki Equatorial Guinea da Gabon.

Sauran kuwa sune Mali da Guinea da Zambia da Morocco da Senegal da kuma Burkina Faso.

Nijer da Ivory Coast da Ghana da Angola da Botswana da Libya da Sudan da kuma Tunisia sune sauran kasashen zasu shiga gasar.

Sai dai manyan kasashen kamarsu Nijeriya da Afrika ta Kudu da Kamaru da kuma Masar ba zasu halarci gasar ba.

Daga ranar 21 ga watan Junairu zuwa 12 ga watan Fabarairu na 2012 za ayi gasar.