Cleverley ya sabunta kwangilarsa a United

tom
Image caption Tom Cleverley

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya yi maraba da amincewar Tom Cleverley na kulla sabuwar kwangilar shekaru hudu a Old Trafford.

Dan wasan mai shekaru ashirin da biyu yana murmurewa ne daga rauni a kafarsa.

Ferguson yace"Tom matashi ne dake da makoma me kyau a kwallon Ingila".

Cleverley ya soma bugawa United a watan Agusta lokacin wasan Community Shield da suka doke Manchester City daci uku da biyu.

Kocin Ingila Fabio Capello ya taba gayyatar Cleverley cikin tawagar 'yan kwallon kasar amma kuma bai samu damar bugawa ba.