An yiwa 'yan kwallon Nijer gagarimar tariya

nijet Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan kwallon Mena

An yiwa tawagar 'yan kwallon Nijer gagarimar tariya a daren ranar Lahadi da suka dawo daga Masar bayan samun gurbin zuwa gasar cin kofin Afrika a karon farko a tarihin kasar.

Duk da cewar Nijer ta sha kashi a wajen Masar daci uku da nema, amma ita ce tafito akan gaba daga rukunin G a saman Afrika ta Kudu da Saliyo.

Magoya baya sun jira su a filin saukar jiragen sama suna rera wakoki suna ta kada-kade.

Wani mai goyon bayan Mena , Abdoulaye Maman yace"Na rasa abinda zan ce, ina cikin murna matuka".

Take daga filin saukar jiragen sama, aka jagoranci tawagar Mena zuwa fadar shugaban kasar Mahamadou Issoufou.

Kuma shugaba Issoufou ya jinjinawa 'yan kwallon.