Corinthians na sha'awar sayen Tevez -Edu

tevez
Image caption Carlos Tevez

Darektan dake kula da kwallon kafa a Corinthians,Edu ya tabbatar da cewa kulob din nada sha'awar sayen Carlos Tevez.

Sakamakon rashin jituwa tsakanin Tevez da kocinsa Roberto Mancini, aka fara jita jitar cewar Tevez din zai koma Corinthians.

Edu wanda a baya ya shaidawa BBC cewar basu da shirin sayen Tevez, ya gayawa Sky Sports News cewar watakila ya dakko Tevez daga Ingila.

Edu ya kara da cewar ya gana da wakilin Tevez, Kia Joorabchian a London.

Edu wanda ya taka leda a Arsenal ya ce akwai wuya dan kwallo yaji dadin zama a Ingila.