Anzhi Makhachkala na zawarcin Van Persie da Anelka

Robin van Persie
Image caption Robin van Persie ya na taka rawa sosai a Arsenal

Kocin Anzhi Makhachkala na Rasha Roberto Carlos, ya ce mai yiwuwa kulob din ya nemi sayen kyaftin din Arsenal Robin van Persie.

Kocin dan kasar Brazil ya kuma ambaci dan wasan Chelsea Nicolas Anelka da na Santos Neymar a jerin 'yan kwallon da suke hari.

"Muna son mayar da kulob din ya zamo kamar Real Madrid ko Barcelona," kamar yadda Carlos ya shaida wani shirin talabijin na kasar Faransa Canal Football Club.

Anzhi ta sayi Samuel Eto'o daga Inter Milan a watan Agusta, inda albashinsa ya haura fan miliyan 8 a shekara.

Dan wasan gefe na Chelsea Yuri Zhirkov da na PSV Eindhoven Balazs Dzsudzsak su ma sun koma kulob din a kwantiragi mai tsoka.

Roberto Carlos ya yi amannar cewa shugaban kulob din - hamshakin dan kasuwa Suleyman Kerimov zai ci gaba da farautar manyan 'yan kwallo na duniya zuwa kulob din.

"Nene daga PSG da Van Persie na Arsenal sune 'yan wasan da muke zawarci. Da kuma Neymar? Na yi magana da shi.

"Idan Real, Barca ko Manchester United ba za su iya sayensa ba, to mu za mu iya. Suleyman Kerimov zai iya bashi abinda ya ke so."

Karin bayani