CSKA Moscow ta sallami Chidi Odiah na Najeriya

odiah Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chidi Odiah

Kungiyar CSKA Moscow ta Rasha ta sallami dan kwallon bayan Najeriya Chidi Odiah.

Kocin CSKA Leonid Slutsky ya bayyana cewar an sallami dan kwallonne saboda batun dokar kayyade yawan 'yan kasashe waje a kulob din.

Yace"Muna saran dan kasar Rasha ne zai maye gurbinsa".

Odiah mai shekaru 27 ya koma kulob dinne a shekara ta 2004 daga Sherrif Tiraspol inda ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar kwallon Rahsa sau biyu da kuma na Uefa a shekara ta 2005.

Amma kuma dan kwallon yayi ta fama da rauni abinda ya hanashi kwantar matsayinsa a kulob din.