Masar ta fasa daukar bakuncin kwallon kafa

london
Image caption A London za ayi gasar Olympics na 2012

Masar ta fasa daukar bakuncin wasannin share fagen buga kwallon kafa a gasar Olympics mai zuwa.

An shirya kasashe takwas zasu fafata a birnin Alkahira daga ranar 26 zuwa 10 ga watan Disamba, inda kasashe uku na farko zasu tsallake zuwa gasar Olympics da za ayi a London a badi.

Masar ta shaidawa hukumar kwallon Afrika cewar ta dauki matakinne saboda zabuka majalisar dokokin kasar dake tafe.

An yawan samun tashin hankali a Alkahira cikin 'yan kwanakin nan.

Kawo yanzu dai CAF bata baiwa Masar amsa ba akan batun.

Baya ga Masar sauran kasashen da zasu fafata a gasar sune Algeria, Gabon, Ivory Coast, Morocco, Najeriya, Senegal da kuma Afrika ta Kudu.