West Brom ta karyata batun yiwa Odemwingie tiyata

osaze
Image caption Osaze Odemwingie

Kocin West Bromwich Albion Roy Hodgson ya karyata rahotannin dake cewar za a yiwa dan kwallon Najeriya Osaze Odemwingie tiyata a gwiwarsa.

Rahotanni sun nuna cewar kocin Super Eagles Samson Siasia ya bayyana cewar za a yiwa dan wasan tiyata nan bada jimawa ba.

Amma kuma Hodgson ya bayyana cewar ba haka lamarin yake ba, amma dai Odemwingie zai tafi Netherlands don ya gana da wani kwararren likita.

A cewar Hodgson "babu batun yiwa Peter tiyata".