Rooney da Capello sun rubutawa Uefa wasika

capello
Image caption Fabio Capello da Wayne Rooney

Ana saran Wayne Rooney da kocin Ingila Fabio Capello zasu rubutawa Uefa wasika a ranar Laraba akan batun jan katin da aka baiwa Rooney din a wasansu da Montenegro na ranar Juma'a.

Watakila a dakatarda Rooney a gasar kofin kasashen Turai wato Euro 2012 saboda tokarin Miodrag Dzudovic, amma kuma ana saran wasikar zata iya kawo sassauci akan hukuncin da za a yiwa dan wasan.

Kakakin Uefa ya shaidawa BBC cewar ba zasu bude wasikar ba, sai a ranar Alhamis idan za a saurari batun.

Yin wasika daga wajen 'yan kwallo da masu horaddasu abune da aka saba yi don kariya a kwamitin ladabtarwar Uefa.

Tabbas dole ne a dakatar da Rooney na wasa guda kuma akwai yiwuwar dakatarwar takai na wasanni uku.