Venezuela ta doke Argentina da ci 1-0

Venezuela ta doke Argentina da ci 1-0
Image caption Wannan ne karo na farko a tarihi da Venezuela ta doke Argentina

Dubban 'yan kallo ne suka cika filin wasa na Estadio Anzoategui a Venezuela domin ganin yadda kasar ta doke Argentina da ci 1-0 a karon farko a tarihi.

Fernando Amorebieta ne ya zira kwallon wacce ta baiwa Venezuela damar lashe wasan - wanda shi ne na biyu a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta 2014 na yankin Kudancin Amurka.

Venezuela ta lashe wasan ne duk da irin kokarin da manyan 'yan wasan Argentina irinsu Gonzalo Higuain da Lionel Messi da Pablo Zabaleta suka yi na ganin sun zira kwallo.

Babu shakka wannan sakamakon zai bakantawa Argentina rai ganin yadda ta lallasa Chile a karshen mako.

Yayin da a gefe guda zai kara wa Venezuela kwarin gwiwa - kuma zai zamo wani abu da ba za a manta da shi a tarihi ba.