Za a yi sauye-sauye a fagen kwallon Ingila

Hukumar FA ta Ingila Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hukumar FA ta Ingila na da tarihi a fagen kwallon kafa

An baiwa Hukumar kwallon Ingila FA wa'adi ta gabatar da sauye-sauyen da za su kawo raguwar basukan da ake bin kulob-kulob na kasar ko ta fuskanci fushin gwamnati.

Tun da farko 'yan majalisar dokoki sun nemi a gudanar da sauye-sauye kan yadda ake gudanar da harkokin kwallon kafa a Ingila.

Kuma yanzu an baiwa FA wa'adin 29 ga watan Fabreru da ta sauya shugabannin gudanarwarta, sannan a fito da sabbin hanyoyin bayar da izini ga kulob-kulob.

"Jagorancin kwallon kafa ya gaza wajen tafiya kafada-da-kafada da wasan na zamani," a cewar Ministan wasanni Hugh Robertson.

"Idan FA ta kasa shawo kan wannan matsalar da kanta, to gwamnati za ta kafa dokoki. Ba na son hakan ya faru, domin kamata ya yi 'yan wasa su gudanar da harkar wasa ba gwamnati ba.

"Wannan wa'adi ne da lallai sai sun bi shi sau-da-kafa domin kawo sauye-sauyen da za su nuna cewa suna son aiwatar da sakamakon wannan rahoton."