Uefa ta dakatar da Rooney wasa uku

Uefa ta dakatar da Rooney wasa uku Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A gasar cin kofin duniyar da ta gabata ma an baiwa Rooney jan kati

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai Uefa, ta dakatar Wayne Rooney wasa uku sakamakon jan katin da aka bashi a wasan Ingila da Montenegro.

Wannan na nufin dan wasan na Manchester United ba zai taka leda a wasannin zagayen farko da Ingila za ta buga ba na gasar cin kofin Euro 2012 da za a yi a kasashen Poland da Ukraine.

Sanarwar da Uefa ta fitar ta ce "kwamitin da'a na Uefa ya dakatar da Rooney wasa uku biyo bayan korar da aka yi masa a wasan share fagen shiga gasar Euro 2012 da Ingila ta fafata da Montenegro ranar Juma'a."

Sai dai BBC ta fahimci cewa hukumar kwallon kafa ta Ingila FA za ta daukaka kara kan hukuncin.

Ana la'akari ne da rahoton da alkalin wasa ya gabatar da kuma wakilcin dan wasan da hukumar kula da kwallon kasarsa da kuma tarihinsa kan rashin da'a.

Karin bayani