Ina bukatar karin lokaci a Super Eagles-Siasia

siasia
Image caption Samson Siasia

Kocin Najeriya Samson Siasia ya nemi afuwa tare da kiran cewar a bashi karin lokaci a cikin aikinsa.

Super Eagles ta kasa tsallakewa zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika da za ayi a 2012, kuma hukumar kwallon kasar NFF na tattaunawa a ranar Alhamis don yanke hukunci akansa.

Amma Siasia ya shaidawa BBC cewar"Ina son aiki na, na san abinda nake yi ina bukatar lokaci ne kawai".

Kocin kuma yayi kokarin kare aikin da yayi cikin watanni goma da aka bashi yana jagorancin Super Eagles.

Ya kara da cewar"ya kamata 'yan Najeriya sun sani cewar muna aiki sosai, muna samun cigaba".

A cewar Siasia akwai 'yan wasan dake kokarin kwace tawagar,"'yan wasan dake bamu matsala sun shafe fiye da shekaru biyar a tim din".

Wani jami'in hukumar kwallon Najeriya NFF, Emmanuel Ikpeme ya ce babu wani kocin Najeriya da aka taba baiwa goyon bayan kamar Siasia.