Ba a yiwa Tevez adalci ba - Mascherano

Carlos Tevez Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Carlos Tevez na cikin tsaka mai wuya

Tsohon dan wasan Liverpool Javier Mascherano ya ce sukar da ake wa takwaransa na Argentina kuma tsohon kyaftin din Man City Carlos Tevez ta wuce gona-da-iri.

Tevez na fuskantar hukunci bayan da aka zarge shi da kin amincewa ya buga wasan Manchester City da Bayern Munich daga benci.

"Tevez ya taka rawa sosai a Man City, don haka ina ganin abinda suke masa yanzu ya yi muni," a cewar Mascherano, kamar yadda ya shaida wa wata jaridar Argentina Clarin. "Abinda ke faruwa yanzu ya bani mamaki matuka.

"Kowa sukarsa ya ke yi, duk da cewa ba ya iya kare kansa. Wannan rashin adalci ne.

"Sai dai Ingila kasa ce mai wuyar sha'ani, idan lamari irin wannan ya afku, kowa sai ya soke ka."

Tevez bai sake taka leda ba tun lokacin da abin ya faru, kuma koci Roberto Mancini ya ce ba zai kara saka shi a wasa ba.

A yanzu dai ya koma horo bayan dakatarwar da aka yi masa ta makwanni biyu, kuma akwai yiwuwar ya fuskanci hukunci kamar yadda kulob din ya bayyana.