FA na binciken kalamai tsakanin Evra da Suarez

suarez da evra Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Luis Suarez da Patrice Evra

Hukumar kwallon Ingila wato FA za ta binciki zargin da dan kwallon Manchester United Patrice Evra yayi akan cewar dan wasan Liverpool Luis Suarez yayi masa kalaman wariyar launin fata.

Evra ya ce lamarin ya auku ne a wasan da suka tashi kunen doki a ranar Asabar.

Kakakin Liverpool ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Press Association cewar Suarez ya karyata zargin.

Sanarwar da FA ta fitar ta ce"An bayyanawa alkalin wasa Andre Marriner zargin bayan kamalla wasan, shi kuma ya kai kara zuwa FA".

Sanarwar ta kara da cewar"FA ta soma binciken lamarin".

Evra yace Suarez ya fada masa kalamin har sau goma.

An tashi daya da daya a wasan da aka buga a filin Anfield inda kyaftin din Liverpool Steven Gerrard ya ci kwallo daya a yayinda Javier Hernandez ya farkewa United.