La Liga:Messi da Higuan sun haskaka

messi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lionel Messi

Lionel Messi ya ci kwallaye biyu sannan Xavi Hernandez yaci daya a wasan da Barcelona ta lallasa Racing Santander daci uku da nema a wasan gasar La Liga da suka buga a filin Nou Camp.

Wannan nasarar ta tabbatarwa da Barca din cigaba da jagoranci akan tebur.

A Santiago Bernabeu, Gonzalo Higuan ne ya zamo zakara a wasan da Real Madrid ta casa Real Betis daci hudu da daya.

Har yanzu Real ce ta biyu akan tebur.

Sakamakon wasu daga cikin karawar karshen mako a La Liga: *Mallorca 1 - 1 Valencia *Getafe 0 - 0 Villarreal *Granada 0 - 0 Atl├ętico Madrid *Rayo Vallecano 0 - 1 Espanyol *Real Zaragoza 2 - 0 Real Sociedad