Murray ya lashe gasar Shanghai Masters

murray
Image caption Andy Murray

Dan Birtaniya Andy Murray ya lashe gasar Shanghai Masters bayan ya doke David Ferrer a wasan karshe.

Murray ya casa Ferrer ne da seti biyu a jere wato 7-5, 6-4.

Dan Birtaniya din a wannan watan ya lashe gasa uku a nahiyar Asiya kadai.

Murray tuni ya lashe gasar Japan da Thailand Open.

Yace" Babu tabbas zan kasance na uku, har sai na samun nasara a wasu wasanni.

Jerin manyan 'yan Tennis a duniya:

1 Djokovic, Novak (Serbia) 2 Nadal, Rafael (Spaniya) 3 Federer, Roger (Switzerland) 4 Murray, Andy (Birtaniya) 5 Ferrer, David (Spain) 6 Soderling, Robin (Sweden)