Van Persie ya ciwa Arsenal kwallaye biyu

Robin van Persie
Image caption Robin van Persie

Robin van Persie ya ci kwallaye biyun da suka taimakawa Arsenal ta samu galaba akan Sunderland a filin Emirates.

Kyaftin din Gunners ya ci kwallon farko ne a cikin dakikoki 29 da fara wasan sannan kuma ya zira ta biyu ana sauran minti takwas a tashi wasan.

Sebastian Larsson na Sunderland ne ya farkewa kulob din kwallo daya a minti talatin.

A yanzu Arsenal ta koma matsayin na goma kenan akan tebur.

Sakamakon sauran wasanni na aka buga a gasar premier:

*Liverpool 1 - 1 Manchester United *Manchester City 4 - 1 Aston Villa *Norwich City 3 - 1 Swansea City *Queens Park Rangers 1 - 1 Blackburn Rovers *Stoke City 2 - 0 Fulham *Wigan Athletic 1 - 3 Bolton Wanderers *Chelsea 3 - 1 Everton *West Bromwich 2 - 0 Wolverhampton *Arsenal 2 - 1 Sunderland