Wydad Casablanca za ta hadu da Esperance

wydad
Image caption Tawagar Wydad Casablanca

Kungiyar Wydad Casablanca ta samu gurbin zuwa wasan karshe na gasar zakarun Afrika bayan ta tashi babu ci tsakaninta da Enyimba ta Najeriya.

A bugun farko dai Wydad ta doke Enyimba daci daya me ban haushi.

A yanzu Wydad din zasu hadu ne da kungiyar Esperance ta Tunisia bayan da Esperance ta casa Al Hilal ta Sudan daci uku da nema.

Esperance ce ta lashe kofin a shekarar 1994, sannan kuma an doke ta har sau uku a wasan karshe.

Za ayi wasanne a farkon watan Nuwamba.

Duk kungiyar data lashe gasar zata samu kyautar dala miliyon daya da rabi, sannan itace zata wakilci Afrika a gasar kulob kulob ta duniya da za ayi a Japan.