Masu kulob suna son a sauya tsarin Premier

premier
Image caption Kusan rabin kulob din Ingila na hannun 'yan kasashen waje

Yawancin kulob din gasar premier ta Ingila wadanda masu mallakarsu 'yan kasashen waje ne suna bukatar a cire tsarin nitsewar kulob daga matakin farko zuwa na biyu, kamar yadda Cif Richard Bevan na kungiyar masu horadda 'yan kwallo ya bayyana.

Bevan ya ce idan har aka samu karin kulob da suka koma hannun 'yan kasashen waje, tabbas zasu iya samun kuri'un da suke bukata don a sauya tsarin.

Amma mahukunta gasar ta Premier sunce tsarin nitsewa da kuma hayewa mataki na gaba suna cikin ka'idar gasar sannan matakin na kara karfin gasar.

A cewar Bevan binciken da majalisar dokokin Birtaniya keyi akan batun harkokin kwallon kafa zasu taimaka wajen hana wannan tsarin da masu kulob din ke tunani.

Kusan rabin kungiyoyin Premier 20 suna karkashin ikon mutanen kasashen waje ne.

A kakar wasan data wuce ne Blackburn tabi sawun Manchester United, Manchester City, Liverpool da Chelsea na komawa hannun 'yan kasashen waje.

Kungiyoyin gasar Premier mallakar mutanen kasar waje:

* Aston Villa (Randy Lerner) * Blackburn (Venky's Group) * Chelsea (Roman Abramovich) * Fulham (Mohamed Al Fayed) * Liverpool (Fenway Sports Group) * Manchester United (Glazer family) * Manchester City (Sheikh Mansour) * Sunderland (Ellis Short) * QPR (Tony Fernandes)