Ban damu da jinkirin van Persie ba - Wenger

van Persie Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Robin van Persie ya zira kwallaye bakwai a kakar bana

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce bai damu da jinkirin da Robin van Persie ke yi wajen sanya hannu kan sabuwar kwantiragi a kulob din ba.

Kwantiragin kyaftin din mai shekaru 28, za ta kare ne a shekara ta 2013, amma ya nace cewa "hankalinsa na kan kulob din".

Wenger ya ce: "Idan ka mayar da hankali dari-bisa-dari har zuwa ranar karshe ta kwantiraginka, wannan shi ne abinda zan dauka mayar da hankali.

"A gani na sanya hannu kan doguwar kwantiragi ba shi ne mayar da hankali ba. Ya san abin da muke so mu tattauna a kai { sabuwar kwantiragi}."

Dan wasan na Holland ya kara nuna kansa bayan da ya zira kwallaye biyu a wasan da Arsenal ta doke Sunderland da ci 2-1 a ranar Lahadi.

Ana dai alakanta shi da tafiya Manchester City, wacce tuni ta sayi Samir Nasri da Gael Clichy daga Arsenal a kakar bana.

"Duka muna bukatar ganin kwararrun 'yan wasa na musamman kuma shi ya na daga cikinsu," a cewar Wenger.

Karin bayani