Ina saran sabunta kwangila ta -Abidal

abidal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Abidal da Messi

Dan kwallon Faransa Eric Abidal ya sanarda cewa yana saran sabunta kwangilarsa a Barcelona, nan bada jimawa ba.

A karshen kakar wasa ta bana ne kwangilar Abida zata kare a Nou Camp.

Yace "Ina saran kulla yarjejeniya saboda ina son in cigaba da zama a nan, wato kulob din da yafi kowanne a duniya".

A cewarsa"A gaskiya bamu cimma matsaya ba akan sabuwar kwangila".

Abidal na saran a bashi wata kwangilar ta shekaru biyu masu zuwa.

A ranar Alhamis ne wakilin Abidal wato David Venditelli zai tattauna da Barcelona akan batun kwangilar.